MALAMI UBAN KARATU

Ilimin shine gishirin zaman danuyi, kuma sinadarine na neman daya duniyar. Gaata ne babba ga dukkan wanda Ya mallaki ilimi, kuma qa'idace dole a ya'data ga dukkan mabukata. A yau malami yazama tamkar juji, wanda bashi da daraja, wannan kuwa babban kuskurene, matukar munki daukaka malami da bashi darajar da yakamaceshi, toh lalle akwai matsala.
Malami shine wanda yake kokarin koyarda kai abinda baka sani ba, ba kataba sani ba, ka manta, kuma Ya tunatar da kai. Malami shine wanda yake horar da kai yadda zaka more rayuwa, yadda zakaci alfanun ilimi.
Malami shine wanda kafi ganinsa a Kodak yaushe, ganinsa shine mafi sauki. Malami shine wanda zaiyi maka bayanin duk wani abinda Ya shige maka duhu, tare da kawo misalai masu inganci.
Malami shine yake raba gardama, Ya sasanta, Ya bada shawara, abin koyi, yana taka rawar iyaye da shugaba. Daraja Malami yanadaga cikin abinda ke daukaka Dan Adam, Ya bashi kamala da nagarta a ko da yaushe.
Mu karrama malamanmu domin hakan zai sa su jajirce wajen bad gudunmowarsu ga ilimi. Matasa sune suke daukan kaso mafi rinjaye a duniya baki daya, ilimi ne zaisa su kasance masu kaifin basira,  zurfin tunani da dogaro da kai. Idan akasamu ilimi ya bunkasa, toh lalle matasa ne zasufi anfana da ita.
Malami kullum cikin kara ilimi yake da anfani da ilimin, bada mahimanci ga al'amuran ilimi zai taimaka wajen tafiyad da al'amuranmu na yau da gobe bisa tsari.

Comments

Popular Posts