Illar raunin megida

Allah Shine kadai adili, duk kokarinda zakayi wajen sulhu musanman GA ma'aurata, sai dai ka basu hakuri, amma ba zaka iyaba. Shi aure, idan har raunin megida ya bayyana a fili, toh agaskia saidai gyaran Allah.
Mace duk tarbiyanta, idan har akayi rashin sa'a ta auri mara ilimi, marasa tarbiya, lalle rayuwatta na cikin hatsari. Dominko, baiyi ibada ba, balle ya tunatar da ita, be kula da dabi'antaba balle ya damu da cewar zata gurbata tarbiyan 'ya'yansa.
Ina kira ga iyaye, da su sa ido akan tarbiyan yara maza, su zama jurumai magidanta masu sanin ya kamata, da kyakyawan rikon iyalansu.
Maata dayawa suna zaman 'ya'yansu ne a gidanjen aurrensu. Allah Ya kyauta.

Comments

Popular Posts