Dan Zaki

Tarbiyan 'da namiji, nada matukar wahala kwarai, jajircewa ta hanyar kula da duk wata dabi'a da zai gurbata tarbiyansa ya zama dole ayi. A hakikanin gaskia, 'da namiji magaji ga mahaifinsa, wadda  shima a gaba zai zama mahaifi kuma maigida. Shi 'da namiji mai tsare mutuncin en uwansa maata ne,Ya basu kariya wajen nuna jarumta, kwazo da hazaka.
A kullum so ake a 'Da miji ya kasance mai gudanar da al'amuransa tamkar zaki, wanda baya barin iyalansa cikin kunci da wahala. Mafi akasarin samari musanman a wannan zamani, na fama ne da matsala ta batar basira wajen bata lokaci, da kuma kayen maye. Suddabaru ne irin na mugum mutum, ya kirkiro domin sauye tunanin matasan nan wajen hanasu hangen nesa da zurfin tunani. Shawo kan wannan matsala abu ne sauki, matasa su sani cewa rayuwa zata kare, ko anki ko anso, tsufa ma ta ishi mutum misali.
Ayi kokari a nemo ilimi do hikimar neman arziki, Allah Subhannahu wa ta'ala Ya wadata dukiya a baynar duniya, nemota kawai za ayi wajen anfani da ilimi musanman na zamani.
Matasa Ya kamata su sauye tunanin su na ganin 'Ya mace tamkar abin wulakantawa, bisa ga tsari da magabata da malammai su ka bayyana, itace 'Ya mace abinsone, abin kauna kuma abin tausayawa. Kuluwa da ita Ya zamo aikine da Ya wajabta akan akan shi 'da namiji. Walau mahaifinta, mijinta, 'dan uwanta ko 'danta. Ina kira ga iyaye, da su kokarta wajen kula da tarbiyan 'ya'yansu, Allah Ya bamu iko baki daya amin.

Comments

Popular Posts