Marasa Gaata

Matsalar tabun hankali nadaga cikin abinda da ke bani tsoro, masu fama da wannan larura abin tausayawane kwarai dagaske. Kalubalantar Kulawa da irinsu, na bukatar hakuri da juria, domin bazasu iya taimakawa kansu ba a cikin wannan yanayi, kamawa daga Kulawa da tsaftar jikinsu, abinda zasuci, kewaye, dadai sauransu.
Bayin Allah masu wannan larura ta tabun hankali na bukatar taimakon en uwansu, al'umma da kuma gwamnati baki daya.        
Yana daga cikin gudunmawar da zamu bada, idan har muka dauki nauyin kulawa da masu larurar tabun hankali, farawa da wanda suke cikin unguwanninmu, musanman marasa galihu, wanda sai kagansu ko tufafi babu, suna zaune cikin juji, wanda idan har sun samu kula, kilama su warke daga wannan cutar.
Babancin tsakanin wanda suke asibiti (psychiatric ) da wanda suke watangaririya a gari, shine gaata. Mu kula da tsaftarsu, abinda zasuci, da kuma lafian jikinsu. Kada mujira sai gwamnati ta kawo musu dauki, muma da kanmu zamu iya. Ya kamata mu had a karfi da karfe domin ganin mun bada irin namu gudunmowa wajen wannan taimakon, ataikaice, taimakekeniyane agaremu baki daya.
Mu sani cewa, yana daga cikin abubuwanda suka jawo tabarbarewar tarbiya a cikin al'ummarmu a yau, wato rashin kula da tausayawa juna. Allah Ya bamu ikon, amin.

Comments

Popular Posts