DABI'UN DA BA NAMUBA
A kullum burin Dan Adam shine ya kasance wayayye. Kokari yake ya hada kansa da halitta, ko dabi'a da yafi kowa a duniya. Mutane sukan manta da matsayinda Allah Subhanahu WA ta'ala Yayi musu, sukan kwaikwayi dabi'ar da mafi akasari kan kaisu GA halaka. 
Idan muka duba, zamuga cewa mu da gaatanmu, munada al'ada, munada tarbiya kuma munada addini. Sai dai kash... garin kwaikwayo al'adun da ba namu ba, mukan zubda namu, mu canza da abinda ba alkhairi bane a garemu.
Duk mutumin da Allah Yayi masa hankali da tunani, toh lalle Yayi kokarin tantance duk wani abinda zai kwaikwayo. Yayi kokari ya auna a minzalin yarbiya, ya tabbatar cewa bazai zamo illa ga al'ummarsa ba.
Duk mutum be ma kai tara ba, muyi kokari mu gyara halayenmu mu ki abinda zai gurbata tarbiyan 'ya'yanmu, mu roki Allah Ya bamu ikon aikata dai dai. 
YA Allah YA San dalilin da yasa Yayi mu a cikin wannan zamanin, Ya Allah Ya bamu ikon gyara halayenmu da sure marasa kyau, mu gyarata da wadda zai an fine mu baki daya. Amin.

Comments

Popular Posts